TARIHIN MUMTAZ MAHAL


 ‎*WACE CE MUMTAZ MAHAL?*


‎Kafin ta zamo shahararriyar sarauniyar daular Mughal, sunan Mumtaz Mahal Arjumand Banu Begum. An haife ta a garin Agra, kuma iyayenta sun kasance mutanen Farisa masu daraja da ƙima. Ƴa ce ga Abu'l-Hasan Asaf Khan, wani shahararren mutumin kirki ɗan Farisa wanda yake da matuƙar tasiri a daular Mughal. Shahararta ta fara a lokacin da aka yi mata baiko da Shah Jahan a 1607. A lokacin tana da shakaru 14 kacal a duniya, in da shi kuma yake da shekaru 15. An ɗora musu aure bayan shekaru biyar da baikonsu a shekarar 1612 a birnin Agra mai ɗinbin tarihi.


‎Ƙayatuwar da Shah Jahan ya yi da kyawu da halayenta ne ya sanya ya ba ta matsayin Mumtaz Mahal, ma'ana 'maɗaukakiyar fadar'. Ana matuƙar son ta saboda kyawunta, da basirarta, da kuma alherinta.


‎Motamid Khan, mai bayar da tarihin masarautar a hukumance, ya bayyana alaƙar da ke tsakanin Shah Jahan da sauran matansa a matsayin irin ta yau da kullum kawai, amma wadda ke tsakaninsa da Mumtaz Mahal na cike da tsananin shaƙuwa, ƙauna, da yarda wadda ta kere ta kere wadda ya yi wa kowane mutum a rayuwarsa.


‎Wani masanin tarihin ya ma bayyana cewa soyayyar da Shah Jahan yake yi wa Mumtaz ta fi ninki dubu na son da yake yi wa sauran matansa, sannan a idonsa, babu wani mahaluki da yi kusa da ita a ƙima.


‎Shah Jahan yana matuƙar girmama hikimar Mumtaz, inda yake neman shawararta a lamurran da suka shafi rayuwarsa da kuma sha'anin mulki. Ta kasance aminiya kuma amintacciyar mai ba shi shawara. Hakan ne ya sanya ta samu matuƙar ƙarfi da tasiri. Mumtaz ta kasance tana zama a kusa da sarkin a cikin Fadar Tattaunawa ta Sirri da Fadar Tattaunawa da Jama'a. Tana kasancewa a ɓoye a bayan wani labule. Idan ta ji wani batu da ba ta aminta da shi ba sai ta ɗora hannunta a kan bayansa, ba tare da an gan ta ba. Ta dalilin cetonta, ya gafartawa maƙiya da dama tare da fasa yanke hukuncin kisa. Yardar da ya yi mata na da matuƙar girma da har ta kai ya ba ta girmamawa mafi ɗaukaka a garin, wato hatiminsa na mulki, wanda yake tabbatar da dokokin mulki a shari'ance, kuma babu wani abu da za a ƙaddamar ba tare da yardarta ba.


‎Mumtaz ta yi zaman aure mai daɗi da Shah Jahan. Ko a lokacin da tana raye mawaƙa sun dinga yabon kyawunta, da alherita, da tausayinta. Duk da yawan ɗaukar cikin da take yi, Mumtaz na  bin tawagar Shah Jahan a gabaki ɗayan yaƙe-yaƙensa na farko. Ita ce ma'abociyarsa a ko da yaushe. A shekaru 19 da suka yi a matsayin ma'aurata, sun haifi ƴaƴa 14 (maza takwas, mata shida), inda bakwai suka mutu a lokacin haihuwarsu ko kuma da suna ƙanana.


‎Zaman aurensu na tsawon shekaru 19 na cike da haɗin gwiwa na musamman, wanda aka gina shi a kan mutunta juna da soyayya ta gaskiya.


‎Allah ya yi wa Mumtaz Mahal rasuwa sakamakon tsananin zubar da jini,a garin Burhanpur a ranar 17 ga watan Yunin 1631, yayin haihuwar ƴarta ta 14, bayan ta yi doguwar naƙuda ta kusan sa'o'i 30. A lokacin tana raka mijinta zuwa yaƙi kan Tudun Dekka. An binne gawarta na wuccin gadi a wani kyakkyawan lambu mai katanga da ake kira da suna Zainabab a Burhanpur. Wani kawun Shah Jahan mai suna Daniyal ne asali ya gina shi a gaɓar Kogin Tapti. Masana tarihin lokacin sun bayyana cewa Shah Jahan ya shiga cikin tsananin baƙin ciki na mutuwar. Sun ruwaito cewa an gaza iya rarrashin sarkin, inda ya shafe shekara a kulle shi kaɗai cikin kewa da baƙin ciki. Bayan ya fito daga kullen kamanninsa duk sun sauya. Furfura ta bayyana, fuskarsa ta yi yaushi, sannan bayansa ya raƙƙwafa.


‎Babbar ƴar Mumtaz ɗin mai suna Jahanara Begum ce ta dinga taimaka wa mahaifin nata a lokacin da yake cikin baƙin ciki, inda ta dinga maye gurbin mahaifiyar tata a lokacin zaman fada.


‎An fara gina Taj Mahal a 1632 sannan aka kammala a 1653, inda dubunnan leburori daga dukkan sassan yankin Asiya suka yi aikin. Shah Jahan ya ƙaddamar da wannan kyakkyawan ginin kabarin domin tunawa da Mumtaz Mahal, inda kuma hakan ya kasance shaida ta soyayyar gaskiya da amana.


‎Mai waƙen nan cikin harshen Ingilishi, Sir Edward Arnold, ya yabi wajen cikin birgewa, in da ya ce "Ba gini ba ne kamar yadda sauran gine-gine suke, tsananin shauƙi ne na soyayyar sarkin aka saƙa a cikin duwatsu." Sau da yawa ana ganin ptsananin kyawun Taj Mahal a matsayin kwatankwacin kyawun Mumtaz Mahal, wanda ya sanya mutane da dama suke bayyana cewa wajen tarihin yana da irin zubin kyawun mace.

Comments

Popular posts from this blog

TARIHIN TAJ MAHAL

HISTORY OF TAJ MAHAL