TARIHIN TAJ MAHAL
TAJ MAHAL
Soyyayar Da Ta Gina Taj Mahal
Taj Mahal! Wani ginin kabari mai matuƙar ɗaukar ido da ban-mamaki da aka gina shi da farin dutse mai sheƙi da santsi a garin Agra na ƙasar Indiya, wanda ya kasance ɗaya daga cikin sababbin abubuwan al'ajabi 7 na duniya.
Sarki Shah Jahan ne ya soma ginin wajen tarihin mai ƙayatarwa a shekarar 1631 domin tunawa da matarsa da yake matuƙar so mai suna Mumtaz Mahal wadda ta mutu a ranar 17 ga watan Yunin waccan shekarar a lokacin da take naƙudar haihuwar ƴarsu ta 14, wato Gimbiya Gauhara Begum. An fara ginin Taj Mahal a 1632, sannan aka kammala ginin baƙi ɗaya a shekarar 1648. Bayan shekaru biyar kuma aka kammala gine-ginen harabar da lambun.
A lokacin da Mumtaz Mahal ta rasu, an fara binne ta a wani kabari na wucin-gadi, sannan daga baya aka mayar da ita Taj Mahal bayan an kammala ginin. Bayan shi ma Shah Jahan ya rasu an binne shi a cikin ginin, gefen kabarinta.
Matuƙar kyawun wajen wanda ke ɓangaren kudu na garin Agra, inda wani katafareren gidan wani shahararren jagora mai suna Raja Jai Singh Na Ɗaya yake ne ya ƙayatar da Sarki Shah Jahan. Hakan ne ya sanya ya zaɓi wajen domin gina mata kabarin, inda shi kuma Jai Singh cikin jin daɗi ya amince suka yi musanya da shi da wata kyakkyawar fada da ke ƙwaryar garin Agra.
Tsarin ginin Taj Mahal ya ƙunshi salon ginin ƙasar Farisa (Iran), da Indiya, da kuma Musulunci, inda ya fitar da wani fasali na daban mai matuƙar kyawu da ƙayatarwa.
Sau da yawa ana kallon Taj Mahal a matsayin alamar soyayya madauwamiya, wanda kyawunsa da kimarsa suke nuna zurfin son da Sarki Shah Jahan yake yi wa Sarauniya Mumtaz Mahal.
A yau, Taj Mahal ya ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin wuraren tarihi da aka fi ziyarta da so a duniya, wanda kuma ya kasance wata alama ko shaida ta ƙarfi da tasirin da so ke da shi a rayuwar ɗan'adam.
Daraini,
1/08/2025.

Comments
Post a Comment