TARIHIN MUMTAZ MAHAL
*WACE CE MUMTAZ MAHAL?* Kafin ta zamo shahararriyar sarauniyar daular Mughal, sunan Mumtaz Mahal Arjumand Banu Begum. An haife ta a garin Agra, kuma iyayenta sun kasance mutanen Farisa masu daraja da ƙima. Ƴa ce ga Abu'l-Hasan Asaf Khan, wani shahararren mutumin kirki ɗan Farisa wanda yake da matuƙar tasiri a daular Mughal. Shahararta ta fara a lokacin da aka yi mata baiko da Shah Jahan a 1607. A lokacin tana da shakaru 14 kacal a duniya, in da shi kuma yake da shekaru 15. An ɗora musu aure bayan shekaru biyar da baikonsu a shekarar 1612 a birnin Agra mai ɗinbin tarihi. Ƙayatuwar da Shah Jahan ya yi da kyawu da halayenta ne ya sanya ya ba ta matsayin Mumtaz Mahal, ma'ana 'maɗaukakiyar fadar'. Ana matuƙar son ta saboda kyawunta, da basirarta, da kuma alherinta. Motamid Khan, mai bayar da tarihin masarautar a hukumance, ya bayyana alaƙar da ke tsakanin Shah Jahan da sauran matansa a matsayin irin ta yau da kullum kawai, amma wadda ke tsakaninsa da Mu...